[go: up one dir, main page]

Jump to content

Kasuwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
wata babban kasuwa mutane nata kaida-kawo suna saye-saye
mutane na cin kasuwa
wata babban kasuwa anata hada-hadar kasuwanci
kasuwa
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na market (en) Fassara, wuri, wuri da kasuwa
Hashtag (en) Fassara Wochenmarkt da Market
an kasa kayan marmari a kasuwa
Kasuwan kifi
wata kasuwa

Kasuwa, wani keɓantaccen guri ne da ake tanada don haɗuwa a yi cinikayya wato saye da sayarwa. Gurin hada-hadar kasuwanci [1] Wanda ita kasuwa tana haɗa mutane daban-daban daga wurare mabam-banta da ƙasashe daban-daban kuma ita kasuwa kusan komai akwai a cikinta. Jam'in kasuwa shi ne kasuwanni haka kuma wanda yake harkar kasuwanci ana ce masa ɗan kasuwa. Ana yi wa kasuwa kirari da "kasuwa akai maki tilas in an ƙiya a kai maki babu" kasuwanni iri-iri ne akwai kasuwar dabbobi akwai kuma kasuwar hatsi da dai sauran kasuwanni. Akwai kasuwa da ake cinikayya ta cikin ƙasa akwai kuma ta ƙasa da ƙasa.[2]

Bunkasa Tattalin arziki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kasuwa dai baya ga bunkasa tattalin arzikin waɗanda ke yin kasuwancin, tana kuma bunkasa ko taimaka wa gwamnati ta hanyar samun kuɗaɗen shiga ta sigar biyan haraji daga `yan kasuwa. Akan bayar ko haraji a duk sati ko wata ko kuma ya danganta da yadda gwamnati ta tsara za ta rinka amsa a lokacin da ta tsara.