[go: up one dir, main page]

Jump to content

Isuikwuato

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isuikwuato

Wuri
Map
 5°44′06″N 7°30′09″E / 5.73489°N 7.50263°E / 5.73489; 7.50263
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaAbiya
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1930
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 441106
Kasancewa a yanki na lokaci

Isuikwuato karamar hukuma ce dake a Jihar Abia, kudu maso gabashin Nijeriya. Sunan Isu-Ikwu-Ato ya samon asali ne daga wasu zuriyar Igbo, wanda suka fito daga zuriya guda uku wato kabilar Isu, wanda a yanzu tazama karamar hukuma.

'yan uwan uku su ne Imenyi wanda shi ne babba, Oguduasaa kaninsa da 'yar uwar su Isuamawo. Wadannan manyan dangi guda uku wanda suke dauke da al'ummomi daban-daban a cikin kowannensu sun hada da Isuikwuato na yau. Tana da kiyasin yawan jama'a sama da mutane dubu 50,000. Isuikwuato yana da albarkatun kasa kamar Tama da Kaolin.

Layukan mai suna bi ta Isuikwuato kuma an sami fashewar bututun mai wanda yayi mummunar illa ga tattalin arzikin yankin da muhalli. Manyan amfanin gona na kudi a garin su ne dabino da rogo. Kasar da ke Isuikwato tana da sako - sako kuma tana fama da zaizayar kasa, kuma hakan ya bar wasu gurare masu hadari a yankin. Ba su da goyon bayan gwamnati da ake bukata don gina magudanan ruwa a kewaye da ake bukata ba tare da cutar da kasar ba.

Albarkacin tsaunika, garin zai mori ababen more rayuwa na ruwa, domin ruwa yana da muhimmanci a garin Isuikwuato saboda yana da wahalar samu. Isuikwuato gida ne ga jami'ar jihar Abia Uturu.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.