Godwit
Godwit | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | Aves |
Order | Charadriiformes (en) |
Dangi | Scolopacidae (en) |
genus (en) | Limosa Brisson, 1760
|
Godwits yana daga cikin rukunin wasu manyan tsutsaye guda huɗu, masu dogon baki, dogayen ƙafafu waɗannan tsuntsaye sun shahara wajen tashi sama da kuma nisan tafiya. Suna daga jinsin tsuntsun Limosa. Dogayen bakunan su na ba su damar tsatsubo tsutsotsi sosai a cikin yashi na ruwa da cikin taɓo. A lokacin hunturu, suna ƙaura tare inda zasu iya samun abinci da yawa.[1] Suna yawan ziyartar bakin teku, suna ƙaura don kiwo a lokacin rani kuma suna ƙaura zuwa kudu lokacin hunturu. Macen wannan tsuntsaye wato (godwit mai wutsiya) tana tashin kilomita 29,000 km (18,000 mi), wannan tafiyar kilomita 11,680 ba tare da tsayawa ba. A cikin shekarar 2020 wani namijin wannan tsuntsaye yayi tashin kusan kilomita 12,200 ba tare da tsayawa ba, wanda yayi ƙaura daga ƙasar Alaska zuwa ƙasar New Zealand, an gano haka a wani rikodin da akayi a wani jirgin samaA cikin Oktoba shekarar 2022, wani ɗan wata 5, ɗin godwit na maza da yayi ƙaura daga Alaska zuwa Tasmania, balaguron da ya ɗauki kwanaki 11, wanda shima akayi rikodin jirgin sama shima yayi tafiyar mil 8,400 (13,500km)
Ana iya bambanta godwits daga ƙwanƙwasa ta hanyar dogayen bakunan su kai tsaye da kuma tsawon kafafunsu. Matan wadannan tsuntsayen sun fi maza girma sosai.[2]
Wannan nau'in tsuntsu shine wanda yafi kowane irin tsuntsu tashi a duniya, wanda yama fi jirgin sama tashi. Yana tashin kusan sama da kwanaki 10 ba tare da ya tsaya hutu ko cin abinci/ruwa ba.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Bird Completes Epic Flight Across the Pacific". ScienceDaily. US Geological Survey. 17 September 2007.
- ↑ "Limosa Brisson 1760 (godwit)". PBDB.