Ajami
Ajami (عجمى), tsarin rubutu ne na Hausa ta hanyar amfani da haruffan Larabci. Wannan rubutun ya samo asali ne daga lokacin da addinin Musulunci ya shigo kasar Hausa a karni na shida miladiyya. Sai dai kuma, kasancewar kwayoyin sautin larabci sun bambanta da na Hausa musamman tagwayen bakake irin su "gy" da "ts", sai kowanne marubuci ya zamo ya na amfani da tasa dabarar wurin rubutun ajami. Sakamakon haka, ajami yake da wuyar ganewa har ma ake yi ma sa kirari da "gagara-mai-shi".[1]
Ajami | |
---|---|
Type | |
Parent systems |
|